Muna yabawa Wakilinmu a Majalisar Dattijai ……Inji Comrade Danmasani Kiri Kasamma

Tunda muke wallahi ka cire son rai da son zuchiya bamu taba sanatan da yake son Al,umar sa  kuma yake kaunar Al,umma tasa tare da   kwatanta musu  Sosai kamar Sen Ahmad Abdulhamid .

Amman abun mamaki, wai sai gashi  da dama daga  acikin Al,Ummar  na kalubalantar alkhairin da yake saboda basu akama ba. Mu kuwa Muna hangen koda ba Kai akama abuba idan aka ma Al,Uma kaima an Maka tunda duk tare zaku amfana

kaduba Dan karamin musali lokachin da wutar lantarki din birniwa , Guri da  kirikasamma ta samu matsala,  barayi suka yanke mana wayar wutar a kalla mun Kai wata uku  babu wutar  a wannan yankunan babu Kuma labarin gyaran ta . Ta zauna  Yanke  , sai wannan bawan Allah ya bada Aikin gyarawa .  Haka satar da akayi na wayar na farko ma shine  ya gyara.  Karku manta Kuma  muna da Yan majalissun jaha a wannan yankunan guda uku Kuma muna da Yan majalissun tarayya da chiyamomi ko su kujerar su bata taimakon Al,Uma bace da bazasu taimaka su gyara ba

Me yasa komai ya tashi ko a jam’iya ko Kuma a garuruwan hadejia Emirate ba,a tunkarar kowa sai amb Ahmad Abdulhamid malam madori shi Kuma baya duba kowa, saboda  kaunar Al, Umarsa,  Amman babu abun zagi a wurin mutane sama dashi

ya kamata mu zama masu furta alkhairi ga Wanda yayi alkhairi ubangiji Allah ya Saka Maka da alkairi sen Ahmad Abdulhamid malam madori, Muna Jin dadin abinda kake mana , Dan haka Muna maka  fatan alkairi har gobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *