” Karya ake min, Ina Nan Daram a Jamaiyar APC ” ….Gov Badaru Abubakar

Tsohon Ministan Tsaro, Sannan tsohon gwabnan jihar Jigawa Alh Mohammed Badaru Abubakar, ya yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani, Wanda ke cewa yana tattaunawa domin ya koma jam’iyyar African Democratic Congress (ADC)

Tsohon Gwabnan na Jihar Jigawa ya bayyana ikirarin a matsayin mara tushe ko makama, cikin wata sanarwa da tsohon ministan ya sanya wa hannu, ya bayyana sarai cewa rahoton gaba daya karya ne, ba shi da tushe, kuma ya samo asali ne na bata-gari na siyasa. Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya ci gaba da tsayawa tsayin daka ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyyar da ya taimaka wajen kafa ta, kuma amincinsa ga jam’iyyar na nan daram babu ja da baya.
Ya bukaci jama’a da ‘ya’yan jam’iyyar APC da su yi watsi da wadannan rahotanni na karya , yana mai kara jaddada cewa ya kasance dan jam’iyyar mai kwazo kuma ba shi da niyyar barin APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *