Tsohon Gwabnan Jigawa zai sake komawa kotu domin tuhuma

Daga Wakilin mu dake Abuja

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta Najeriya, Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan Jigawa State, Sule Lamido, a ranar Laraba 1 ga Afrilu, 2026, a gaban Mai shari’a Peter Odo Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, domin fara sabon shari’a kan zargin badakalar kudi har Naira biliyan 1.3.
Za a gurfanar da Lamido tare da ‘ya’yansa biyu, Aminu Lamido da Mustapha Lamido, da kuma kamfanoninsu biyu, wato Bamaina Holdings Ltd da Speeds International Ltd. Ana zargin cewa sun aikata badakalar ne ta hanyar karɓar cin hanci (kickbacks) da kuma bayar da kwangilolin bogi, a lokacin da Lamido yake gwamnan Jigawa daga 2007 zuwa 2015.

An ɗaga ranar gurfanar da su zuwa 1 ga Afrilu bayan da ba su halarci kotu ba a ranar da aka fara tsara shari’ar wato Jumma’a 13 ga Maris, 2026.
Lauyan masu kare kansu, Joe Agi (SAN), ya nemi afuwar kotu kan rashin zuwan wadanda ake kara, inda ya ce sanarwar ranar shari’ar ta iso musu ne a makare. Ya kuma yi alkawarin cewa za su halarci kotu a ranar da aka dage shari’ar.

Sai dai lauyan gwamnati, Chile Okoroma (SAN), ya nuna bacin rai kan rashin zuwan wadanda ake kara, yana mai cewa an mika musu takardar sammaci yadda ya kamata kuma cikin lokaci.
Ya kuma bayyana cewa masu gabatar da kara sun rubuta wa Babban Alkalin Kotun Tarayya, John Tsoho, domin a dawo da alkali na farko da ke sauraron shari’ar, Ijeoma Ojukwu, wacce aka sauya aikinta zuwa Calabar, domin ta ci gaba da sauraron shari’ar a Abuja.

Mai shari’a Lifu ya ce wannan batu na gudanarwa ne, wanda Babban Alkalin Kotun Tarayya ne zai yanke hukunci a kansa, sannan ya ɗaga shari’ar zuwa 1 ga Afrilu domin sabon gurfanarwa.
Tun a 2015, EFCC ta shigar da karar a gaban Mai shari’a Ojukwu a Kotun Tarayya ta Abuja, kan tuhuma guda 27

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *