Daga Wakilinmu dake Abuja
Wani Jigo a Jamaiyar PDP daga Karamar hukumar Birniwa ya koma APC ta hannun Sanata Ahmad Malam Madori. Isyaku Sunburtu Wanda aka wanka jigo ne a jam’iyyar PDP ta karamar hukumar Birniwa.
Tawagar maigirma Sanata wadda ta hada da Alhaji Haruna Muhammad (Commander), Hon. Usman Gama Rara, Seena Mallam Madori, Muhammad A Musa da dai sauransu sune suka Kai Sumburtun babban birnin tarayya Abuja domin sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa tsintsiya (APC)
wannan sauya shekar Inji masana harkokin Siyasa a Birniwa na cewar gagarumar nasarace ga jam’iyyar a yankin, dama jiha baki daya.
Muna da Karin bayani kan wannan zama cikin rahotannin mu na gaba
