Sabuwar dokar fidda Yan takarar Jamaiyu a zabe me zuwa

From Our Reporter Ahmad Arab ABUJA

Ana tsammanin fara yin amfani da sabuwar dokar KATO bayan KATO a lokacin zaben fidda gyani na kowaccha Jamaiyar a Nigeria. Domin kuwa ana saran dokar na cikin sabbin Dokokin da shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kansu wadda Majalisar Ƙasa ta tura masa, ta soke tsarin indirect primaries gaba ɗaya daga cikin hanyoyin fidda gwani na jam’iyyun siyasa.

 

Wannan sabuwar dokar ta nuna cewa, jam’iyyu ba za su ƙara amfani da tsarin delegates wajen zaɓen ‘yan takara ba. Yanzu hanyoyi biyu kacal suka rage a hukumance:

 

Direct Primaries: inda duk wani ɗan jam’iyya mai rajista ke da damar kaɗa kuri’a kai tsaye

Consensus: (Yarjejeniyar cikin gida) inda jam’iyya da ‘yan takara ke cimma matsaya ɗaya domin janyewa wani dan takara.

 

Sabuwar dokar na nuna cewa duk ‘yan jam’iyya masu rajista sun zama masu cikakken ikon zaɓe a tsarin direct primary election wato (kato bayan kato) maimakon takaita ikon ga delegates kaɗai.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *