Wata Kungiya Mai suna Danmodi health Ambassadors Dake karamar hukumar Gumel ta bawa jagoran matasan jam’iyyar APC na jahar Jigawa kwamandan Alhaji Salihu Muhammad Atafi lambar yabo. Kungiyar tace hakan ya biyo bayan irin gudunmawar da yake bayarwa ga al’umma a fadin wannan Jiha.
A lokacin taran gabatar da Jawabai inda da yake nasa Jawabin commander Salisu Muhammad ya godewa mutanen ƙaramar hukumar Gumel,bisa karramawa,da kuma kyakkyawar tarbar da ya samu daga garesu.
Kafin karramawar,sai da aka gabatar da Walimar nuna godiya ga Allah,wadda aka shirya wa ɗaya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC,Dr.Abubakar Yahaya(C.U),bisa matsayin Registerer da ya samu,a Federal College of Agriculture Kirikasamma, Jigawa state.
Kafin tashi daga taran Saida Alh Salisu Atafi ya bayar da gudummawar Naira Miliyan ɗaya(1.M),ga ƙungiyar kurame masu goyon bayan Ɗanmodi(GUMEL DEAF SUPPORT FOR DANMODI).
