A lokacinda ake Shirin fafata zaban gwabna a Jihar Ekiti, hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa ta fitar da sunayen Yan takarar neman kujerar gwabnoni daga Jamaiyu Amma Babu Dan takarar a Jamaiyar PDP
Hukumar tace Hakan Yana da nasaba da rigimar waje shugaba a PDP , inda hukumar tace Bata Sami matsaya daga uwar Jamaiyar ba , kan su waye zasu bada Dan takarar daga bangarori biyu na PDPn .
Dan haka Akwai yiwuwar zaayi zaban Banda PDP kenan. Haka Kuma ake saran abun zai faru akan Jamaiyar ko a babban zabe na 2027 matukar suka kasa shawo kan rigimar Kafin lokacin
