Bama Bamai sun fashe a tsakiyar garin maiduguri

Mazauna birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun shiga firgici a yammacin  Litinin 16 Maris 2026 bayan jin ƙarar wasu fashe-fashe masu karfi a bakin kasuwar Monday Market

‎Rahotanni na nuna cewa ana zargin mayakan ƙungiyar Boko Haram da dasa bama-baman a wasu wurare na birnin.

‎Wuraren da lamarin ya shafa sun haɗa da ƙofar asibitin koyarwa na Maiduguri, zagayen kasuwar Litinin, da kuma yankin Elkanemi. Anga maaikatan agaji suna ta jigilar wadanda suka rasu da jikata zuwa asibitocin Jihar a cikin Maiduguri .

‎An ce fashewar farko ta auku ne da misalin ƙarfe bakwai na yamma, jim kaɗan bayan buɗe baki na azumin watan Ramadan.

‎Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da ko akwai waɗanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *