Faida Radio News
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sake jaddada kudurin jam’iyyar na tabbatar da tsarin raba shugabanci na 60/40 tsakanin sabbin masu sauya sheka da ’yan jam’iyyar APC a jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa Yilwatda ya bayyana hakan ne a wata ziyarar da ya kai wa gwamnan jihar Kano Abba Yusuf.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Yusuf, Sanusi Dawakin-Tofa ya fitar, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya yaba da hadin kan da ke tsakanin jam’iyyar tare da bayyana yawan fitowar jama’a a taron da aka gudanar a baya-bayan nan a matsayin abin burgewa, yana mai nuni da cewa jam’iyyar ta kara karfi a jihar.
Yilwatda ya kuma yabawa jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da Alhaji Yusuf Gawuna da Sanata Barau Jibrin bisa goyon bayan manufofin gwamnan.
Ya kuma yaba da gudunmawar da Dr Abdullahi Ganduje ya bayar, inda ya bayyana rawar da yake takawa wajen ci gaban jam’iyyar a matsayin mai kima.
A nasa jawabin, Gwamna Yusuf ya godewa shugabannin jam’iyyar APC bisa wannan ziyara da suka kai masa, ya kuma yi alkawarin ci gaba da hada kai da jam’iyyar domin bunkasa hadin kai da ci gaban Kano.
