Ana ci gaba da bayyana muhibbar Gwabna Namadi da Sen Malam Madori

Jam’iyyar APC na shirin ci gaba da gudanar da mulkinta a jihar Jigawa, biyo bayan irin yanda ake nuna  amincewa kan  shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Umar Namadi da Sanata Ahmad Abdulhamid na majalisar dattawa mai wakiltar Jigawa ta arewa maso gabas domin  duk  sun zarce a karo na biyu wadda wasu masu ruwa da tsaki a yankin Hadejia suka yi.

Hadejia wadda  ta tun ba yauba ta kasance tungar APC tun  kafin zaben 2015.  Domin kuwa  jam’iyyar PDP mai mulki a lokacin ta sha kaye a hannun APC a zaben kananan hukumomin na shekarar 2013a  Hadejia da Malam Madorin .

Tun bayan lashe zaben 2015 jam’iyyar APC ta ci gaba da kallon yankin  a matsayin inda yafi koina  tasiri a cikin jam’iyyar APC a jihar . A tsawon wannan lokaci, Sanata Ahmad Abdulhamid ya zama shine  kashin bayan jam’iyyar a yankin tun ma kafin ya samu mukami na zabe. A kwanakin baya ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da jihar Jigawa ta arewa maso gabas Hon Abdullahi Ango Malam Madori daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar ya yabawa Sen  Ahmad a matsayin “Janar na  siyasar Hadejia,” inda ya bayyana cewa zuri’a za su rika tunawa da irin gudunmawar da ya bayar. Ya fadi haka ne a wajen taron jama’a Wanda wasu kungiyoyin matasa suka shirya domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Umar Namadi da Sanata Malam Madori .

Yayin da zabukan 2027 ke kara karatowa, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Jigawa sun fara sake duba dabarun su na ci gaba da wanzar da jihar daga abin da suka bayyana a matsayin ‘yan siyasar da ke kokarin ruguza APC  mai mulki . A cikin makonni hudu da suka gabata, masu fada a ji a cikin jam’iyyar a Masarautar Hadejia na ci gaba da goyon bayan takarar Shugaba Tinubu, M Umar Namadi da Sen Malam Madori a karo na biyu tare da kara kira ga Sanata Ahmad, wanda kuma ke rike da mukamin Shugaban Kwamitin ‘Yan Sanda na Majalisar Dattawa, ya ci gaba , mutane Kuma su fito domin a karbe shi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC tilo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *