Akwai yiwuwar PDP reshen Jihar Jigawa zata kwatse zuwa wata Jamaiya

  • Taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ya karbi takardar korafi da koke da neman Jagoran talakawa Dr. Sule Lamido CON, da ya nemawa magoya bayansa mafitar siyasa daga Jam’iyyar PDP zuwa wata Jam’iyyar ta daban duba da abinda aka yi masa, yanayin halin da ake ciki da kuma yanayin da za’a iya shiga bayan karewar wa’adin shugabannin Jam’iyyar a ranar 9 ga Disamba.

Tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Jigawa ne suka yi wannan kiran yayin da suka mika takardar korafi da cikakken bayani da makasudin yin wannan kira tare da neman ya lalubo musu mafita siyasa. Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa Dr. Babandi Ibrahim shine ya mikawa jagoran takardar yayin gudanar da taron.

Da yake mayar da jawabi Jagoran ya bayyana irin halin da ake ciki tare da dogon karatu na yadda tsari da yanayin siyasarsa yake yace kuma za’a yi dukkan mai yiwuwa domin gyara matsalar PDP tare da kira a gare su da su yi hakurin jiran abinda zai je ya dawo domin su samo bakin zaren kafin karewar wa’adin shugabannin Jam’iyyar PDP na Kasa ya cika.

Yace taro da aka yi a Ibadan ba taro bane domin babu shi kotu ta hana gudanar dashi, ya ce su kara hakuri a jira aga zuwa karewar wa’adin. Yace a yanzu Gwamnoni suna neman mafita samun bakin zarensu gudun kar su tsaya su je matsala ta shafe su yace su kara hakuri. Da yake amsa tambaya game da ko in lokacin ya cika ba a magance matsalar ba zai bar PDP yace wannan kuma abinda bai zo bane a bari a magance matsalar tukunna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *