Magoya bayan PDP 1335 sun chanza sheka zuwa APC a karamar hukumar Birniwa

 Adamu Rabiu Idris

A yammacin lahdin data gabata ne Hon Sale Ahmad Birniwa mataimakin gwabna na musamman kan harkokin matasa , ya tsara Wani kwarya kwaryan bikin karbar Wani matashi Dan Jamaiyar PDP tare da magoya bayan sa a karamar hukumar Birniwa zuwa cikin Jamaiyar APC

 

Taran wanda ya biyo bayan ganawar da akayi tsakanin matashin Mai suna Isiyaku Sunburtu da Sanatan Jigawa ta arewa maso gabas a ofishinsa dake Abuja , inda ya bashi Kalmar shahadar shiga Jamaiyar APCn bayan tabbatar da barin tsohuwar Jamaiyar tasa ta PDP

 

A lokacin wannan taro shugaban karamar hukumar Birniwa Hon Shehu Baba Wanda shine Mai masaukin baki, ya gayyaci Muhammad Salisu Atafi Wanda akafi Sani da COMMANDA domin karbar wannan Jagoran matasa tare da mutanan sa kimanin 1,335 a harabar gidan karamar hukumar dake Birniwa .

 

Taran ya sami Wakilcin Sanata Ahmad Abdulhamid Wanda Hon Adamu Ibrahim Gire ya wakilta bisa rakiyar sauran mutanan sa. An Kuma gabatar da Jawabai domin karfafa gwiwar sabbin yan Jamaiyar , Wanda shugaban Jamaiyar Mai barin gado M Magaji Matara yayi tare da Kalaman bitar irin ayyukan gwabna M Umar Namadi a yankin kananan hukumomin Birniwa da Kiri Kasamma ta bakin Hon Sale Ahmad Birniwa .

 

Tunda farko Kafin fara taran , Saida tawagar takaiwa Dattijan Jamaiyar Alh Amadu Gurgu ziyarar ban girma a gidansa dake Birniwa tasha .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *