Daga Damaturu , Jihar Yobe
Kungiyar Izala Mai ofishinta dake Jos ta dakatar da tafsirin Ramadan na Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria a Masallacin Mokas, Damaturu, Jihar Yobe, bayan kwanaki 11 da fara gabatar da tafsirin.
Bayanai sun nuna Shugaban Majalisar Mallamai ta Ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayar da umarnin dakatarwar bisa dalilan tsaro. Wannan ya biyo bayan hudubobi da nasihohin da malamin yake yi a wurare daban-daban a Jihar ta Yobe, ciki har da hedikwatar ‘yan sanda da Masallacin Ali marami.
Malamin ya karbi nasihohin da shugaban Kungiyar Sheikh Sani Yahaya Jingir yayi masa kan rashin Kyakkyawan usulubin da yake amfani dashi wajan gudanar da karatuttukan nasa , duba da halin da kasar take ciki a yanzu lokacin da suka gana ranar 14 Ramadan a helkwatar Kungiyar dake Jos, Jihar Plateau
Alkali yace, ya amince da hukuncin da aka dauka akansa , Kuma zai kiyaye gaba
Kawo yanzu dai babu sanarwa a hukumance , kan karatun na Alkali Zaria Wanda yayi a helkwatar ta Yan sanda , ganin irin kausasan Kalaman da Malamin yayi amfani dasu akan shugaban Kasa da sauran shugabani
