Jihar Jigawa ta shiga yarjajjeniyar noman ciyawa

By Muhammad Saidu Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanya Hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan noman wata ciyawar Dabbobi mai Suna Alfalfa domin bunkasa harkokin kiwo, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ne ya jagoranci rattaba hannu kan muhimmin yarjejeniyar da wasu gungun masu zuba jari domin fara noman.

Karkashin yarjejeniyar, Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da bayar da kadada har 100,000 domin aiwatar da aikin.

An rattaba hannun yarjejeniyar ne bayan ziyarar girmamawa da wata babban tawaga karkashin jagorancin Darakta Janar na Hukumar NITDA, Kashifu Inuwa, ta kai Jihar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *