Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Joash Amupitan SAN ya gayyaci kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa karkashin jagorancin Kabiru Turaki da kuma wasu tsaffin ‘ya’yan jam’iyyarmu da ke ikirarin cewa suna da mukaman shugabanci daban-daban a jam’iyyar, a cewarsa, “a nemo hanyar da za a magance rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
Bangarorin biyu sun gabatar da hakikanin gaskiyar lamarin tare da tabbatar da cewa yanzu haka batutuwan na gaban kotun daukaka kara. A karshe shugaban na INEC ya kammala da cewa an kira taron ne domin jin ta bakin bangarorin biyu, duk da cewa hukumar na sane da shari’o’in da ke gaban kotun daukaka kara, kuma hukumar na dakon hukuncin karshe na kotu kan lamarin.
A karshen taron, shugaban jam’iyyar na kasa, Kabiru Turaki SAN ya ce “A matsayinmu na ingantacciyar shugabancin jam’iyyar da ta fito a babban taro (duk da cewa an yi takara a kotu), muna jiran sanarwar kotu, za mu ci gaba da gudanar da ayyukan jam’iyyar adawa, wanda shi ne rike gwamnati a kan muhimman batutuwa kamar tsaro, samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da dai sauransu.
