Hon Makki Yalleman yayi alkawarin bude kwaltar Malam Madori da Kaugama Kafin 31 December 2025

Nan da zuwa sati biyu masu zuwa, ana sa ran zaa gudanar da bikin bude hanyar kwalta wadda ta tashi daga Malam Madori zuwa Kaugama Mai kimanin tsahon 16 km .

Hanyar wadda Wakilin kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama a zauran majalisar tarayya Hon Makki Abubakar Yalleman yake ginawa , an fara ta tun a shekarar ta 2024 , yanzu haka Kuma aikin yakai tsahon kilometre uku .

Hon Makki shine ya bada tabbacin kammalawa da budewa hanyar Kafin Karshan wannan shekara ta 2025 a lokacin taran gwabnati da Jamaa Wanda aka gabatar a karamar hukumar Malam Madori . Hanzu dai sauran kwanaki goma Sha shida Kafin shekarar 2025 ta kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *