Ya Kamata gwabnatin Jihar Kano ta maida hankali kan abinda ya dace

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bukaci Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya daina siyasantar da batutuwan tsaro, ya maida hankali wajen magance manyan matsalolin da ke addabar jihar .

Yayin mayar da martani kan zargin da gwamnatin jihar ta yi cewa kalaman Sanatan na iya kawo cikas ga kokarin tsaro da ake yi, bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ta 34 da Gwamnan ya jagoranta, Sanata Barau ya bayyana cewa matsalolin tsaro a kasar nan , ciki har da abin da ya shafi mamayar ‘yan bindiga a wasu sassan Kano na bukatar hadin kai tsakanin dukkan bangarori domin shawo kansu.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya karyata zargin gwamnatin jihar, yana kalubalantar su da su fitar da bidiyon da yake nuna cewa ya yi wani kalami da zai iya ta’azzara matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *