Gwabnonin Jihohin arewa sun fara damarar tunkarar kalubalen

Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su gudanar da babban taro a Kaduna ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna kalubalen tsaro da ke addabar yankin. Peter Ahemba, hadimin gwamnan Nasarawa kan harkokin jama’a, ya shaida wa Daily Trust cewa za a samu halartar manyan shugabannin gargajiya, tare da fatan taron zai samar da matsaya guda da za ta taimaka wajen inganta tsaro a Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *