Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince wa Jiha karbar bashin #90 Billion

  1. Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince wa Gwamnatin Jiha ta karɓi bashin Naira biliyan 90 daga bankin Zenith, bisa yarjejeniyar cewa Gwamnatin Tarayya ce za ta biya bashin daga rabon ribar kudaden Kamfanin Iskar Gas na Kasa.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, kuma dan majalisa mai wakiltar Roni, Alhaji Lawan Muhammad Dansure, ya tunatar da cewa majalisar ta taba amincewa gwamnatin jiha ta ɗauki wani kamfani na kwararru don bincike da shiga tsakani wajen tabbatar da karɓar kudaden ribar iskar gas da ya tsaya a hannun gwamnati.

A cewarsa, aikin kamfanin ya sa gwamnatin tarayya ta ba jihohi 36 damar karɓar bashi daga bankuna, wanda za a rika biyan sa sannu a hankali cikin watanni 18. Ya kara da cewa karkashin wannan tsarin, Jigawa za ta samu Naira biliyan 256 na ribar kudaden iskar gas.

Dansure ya ce wannan yarjejeniya za ta taimaka wa jihar samun ƙarin kudade don aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al’umma.

Bayan tattaunawa da samun amincewar mafi rinjaye, shugaban majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya sanar da cikakkiyar amincewar majalisar ga bukatar karɓar bashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *