By Muhammad Saed Dutse
Gwaman Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya yi kira ga Alkalai kan su sanya tsoron Allah wajen gudanar da aiyukansu.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya Karbi babbar tawagar Alkalan kotunan shari’ar musulunci na Jihohin Arewacin Najeriya a gidan Gwamnati yayin wata ziyara da kumgiyar Alkalan kotunan shariar musulunci suka kawo masa a ifishinsa .
