Ana ci gaba da gano badakala a hukumomin gwabnatin tarayya

Bayan gano wata mummunar badakala da majalisar tarayya tayi cikin harkokin maaikatar kula da harkokin jin Kai wadda minista Sadiya Umar farouk ta Jagoranta a zamani tsohon shugaban kasa marigayi Muhammad Buhari , Yanzu Kuma wata wadda ta zarce wannan ta taso a cikin hukumar kula da  kamfanin man fetur na kasa NNPCL

Wannan tasa Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ya ba da umarnin a kama tsohon Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, Mele Kyari, saboda rashin bayyana a gabanta kan zargin tara biliyan ₦210 da ba a tantance ba tsakanin 2017 da 2023.

‎A lokacin zaman, wasu ‘yan majalisa sun yi kira ga shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Dankwambo (Gombe North), da ya sake bai wa Kyari damar bayyana, suna masu ambaton rahotannin cewa yana karbar magani a Jamus.

 

A halin yanzu, tsohon Babban Jami’in Kudi na NNPCL, Umar Ajiya Isa, ya yi watsi da ikirarin cewa tara biliyan ₦210 ba a tantance ba, yana mai jayayya cewa adadin ya zarce jimillar kudaden shigar da kamfanin ya samu a lokacin da ake nazari a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *