Kotu Ta Ba Da Umarni A Fara Ba Hausawa da Fulanin Jos Ta Arewa Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Filato
Babbar Kotun Jihar Filato da ke Jos ta yanke hukuncin da ake kallon a matsayin wani babban ci gaba wajen tabbatar da daidaito tsakanin al’ummomin jihar, inda ta umarci Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ta bai wa wata mata Bahaushiya mai suna Fatima Baba Akawu takardar shaidar zama ɗan ƙasa (Certificate of Indigene) cikin kwanaki 30.
Lamarin ya samo asalin ne yayin da wata Bahaushiya mai suna Fatima Akawu wacce aka haifa kuma ta tashi a Jos ta je ƙaramar hukumar Jos ta Arewa karɓar shaidar zama ƴar Jos ta Arewa inda nan take aka hana ta sai aka bata shaidar wucin gadi. Daga nan ta maka ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a kotu.
A hukuncin da Mai Shari’a C. Donglong ya yanke a ranar 9 ga Yunin 2026, kotun ta bayyana cewa takardar “Residential Certificate” da wasu ƙananan hukumomi ke bayarwa ba ta da wani matsayi a dokokin Najeriya, tare da cewa ƙin bai wa Fatima takardar zama ɗan ƙasa yayin da aka bai wa wani ɗan Berom irin wannan takarda ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa.
Kotun ta kuma bayyana cewa duk ɗan da ya fito daga iyaye masu cikakken matsayin ’yan asalin wani yanki yana da haƙƙin samun takardar zama ɗan ƙasar yankin ba tare da la’akari da ƙabilarsa ba. Haka kuma ta haramta wa Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ci gaba da amfani da “Residential Certificate” a matsayin madadin takardar zama ɗan ƙasa.
Masanin shari’a a Jami’ar Sa’adu Zungur da ke Bauchi, Farfesa Ahmed Salisu Garba, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yaƙi da wariya. Ya ce hukuncin ya tabbatar da matsayar cewa bambancin “ɗan asali” da “baƙo” ba shi da tushe a kundin tsarin mulki idan ana maganar haƙƙin ɗan ƙasa.
Farfesan ya yi kira ga gwamnatin jihar Filato da sauran ƙananan hukumomin ƙasar nan da su yi biyayya ga hukuncin kotun tare da dakatar da duk wata hanya da ke hana wasu ’yan Najeriya samun cikakken haƙƙinsu bisa la’akari da ƙabila ko asali.
