A wannan yankin da ake gwabzawa tsakanin kasar Iran da kuma kasashen Yahudu da Nasara wato Israela da Amuruka, da suka dunkule suka tarar wa kasar Iran, akwai salon zamba da amfani na’urorin leken asiri don kai wa Iran hari
Wasu rahotanni sun bayyana cewa Ali Larijani wanda shi ne shugaban rundunonin tsaron Iran kasar Israela ta dade tana farautarsa, inda ta sami nasarar kashe shi a harin jiya Talata, bayan ta sami lambar wayarsa ta wani matashi dan shekara 20 da ya daɗe yana yi wa Isra’ila leken asiri kan Larjani
Isra’ila ta kashe ta hanyar tirakin din lambarsa, inda suka kai masa hari bayan ya je gidan yarsa, suka harba masu makamin da ya yi sanadiyyar kashe shi, tare da ƴar tasa da dansa da kuma wani jami’insa mai tsaron lafiyarsa
