Gwabnan Jihar Jigawa ya Sami lambar Girmamawa kan harkokin Ilmi

By Muhammad Saidu Dutse

Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT) ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da lambar yabo ta Gwamna Mafi Ayyuka a Arewa a bangaren ilimi, inda ta bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa, abin koyi, kuma mai kaunar malamai.

An gabatar da wannan bikin bada lambar yabo ne a Fadar Gwamnati da ke Dutse, a lokacin da tawagar ta Kungiyar Malaman  ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban ƙungiyar na Kasa Kwamared Muhammad Hambali, tare da Shugaban Kungiyar na Jihar Jigawa, Kwamared Abdulkadir Yunusa, da shugabannin Kungiya na jihohi 19 na Arewacin Najeriya, suka kai wa Gwabnan  ziyarar ban girma  a ofishinsa

A lokacin wannan Zama , shugabanin Kungiyar sunyi  bayannan girmamawa tare da nuna Jin dadin Malaman kan irin kulawar da Gwabnan yake bawa harkokin Ilmi a Jihar. Inda Kuma daga bisani Mai Girma Gwabna ya maida Jawabin godiya bayan karbar lambar yabo daga shugaban Kungiyar na kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *